Tsigaggen dan majalisar tarayya ya cusa ayyukan naira miliyan 800 na boge a kasafin kudin 2018

0

An gano cewa tare da Herman Hembe, dan Majalisar Tarayya da a cikin 2017 aka yi harkallar cusa wasu ayyuka a kasafin kudin wannan shekara, ya sake cusa naira miliyan 827 a cikin kasafin kudi na 2018.

An dai kwace wakilcin Kananan Hukumomin Vandeikiya da Konshisha na jihar Benuwai daga hannun Hembe cikin watan Yuni 2017, bayan da Kotun Koli ta tabbatar da cewa ba shi ne halastaccen dan takarar jam’iyyar APC ba a zaben 2015.

Shekara daya bayan korar sa da aka yi, PREMIUM TIMES ta gano cewa, Hembe, wanda na hannun damar Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara ne, ya biyo ta bayan gida an yi daka-dakar cushen ayyuka har na makudan kudade da shi a cikinn kasafin 2018, musammann a cikin kasafin hukumomin gwamnatin tarayya biyu.

Ayyukan dai duk na wala-wala ne, da suka hada da gina titin da ya dangana da har kofar gidan sa a jihar Benue da kuma raba baburan hawa a yankin sa.

Buhari dai ya kai kasafin kudi zuwa Majalisa, watanni biyar bayan tsige Hembe daga kujerar sa. Hakan zai ba mutane mamakin yadda aka yi Hembe ya biyo ta Katanga, ya tsallo har aka yi rabon watandar ayyuka na miliyan 826 da shi, aka kuma cusa su cikin kasafin 2018.

Duk daccewa Buhari ya yi korafin cewa an yi cushen wasu ayyukan, amma bai san cewa har da wani da ba shi da ikon sa baki ko sa hannu a harkar kasafin ba, domin tuni kotu ta tsige shi, kuma ba ya ma majalisar.

Jim kadan bayan tsige shi, sai Buhari ya nada Hembe a matsayin shugaban hukumar gudanarwar Cibiyar Habbaka Ayyukan Kwadago ta Micheal Imodu, a jihar Kwara.

Wannan cibiya bangare ne na Ma’aikatar Ayyukan Kwadago ta Kasa da Samar da Ayyuka.

Wannan hukuma ta na gudanar da ayyukan horaswa da kara kwarewa da ingancin kungiyoyin kwadago, ma’aikatan da ke aiki a ma’aikatar kwadago da sauran su.

A cikin kasafin wannan hukuma ne wanda aikin ta kawai na gudanarwa ne a ofis, amma Hembe ya shiga, ya fita, ya yi kurda-kurdar da aka cusa ayyuka har na naira milyan 652.

PREMIUM TIMES ta gano cewa duk da wannan cibiya a jihar Kwara ta ke, ayyuka 12 daga cikin 18 da gwamnatin tarayya za ta gudanar wa cibiyar, sai duk Hembe ya karkatar da su zuwa garin su da jihar sa.

Daga cikin wasu ayyukan da ya karkatar na cibiyar mai suna MINILS, har da gina titi na naira miliyan 95 daga wata magamar kwalta har zuwa kofar gidan sa a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Titin mai suna kuma da aka fi sani da Nyor Hembe Road, sai aka baddala sunan sa a cikin kasafin kudin zuwa Nyor H Road, don a bad-da-sawu.

Akwai kuma aikin gina burtsatse na sola a garuruwa takwas da ke maabar Hembe, a kan naira milyan 50, sai kuma sayo Babura 100 akan naira miliyan 37.5.

Sauran sun hada da gina ajujuwa, samar da wutar lantarki, gina zaurukan taro, samar da taraktar noma da kuma gina wasu burtsatse, da gaba dayan wannan rukunin ayyuka zai ci naira milyan 465.

Wannan harkalla ta gigita Ma’aikatar Kwadago da Daukar Ma’aikata, musamman ma kakakin yada labaran ma’aikatar, Sam Olowookere, yayin da ya ji wannan labari.

Share.

game da Author