TARO: Za a tattauna matsayin gwamnati game da ayyuka MDGs da suka shafi kiwon lafiya

0

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu za su tattauna matsayin gwamnatin game da ayyukan shirin muradin karni (MDGs) da ya shafi fannin kiwon Lafiya.

Kungiyoyin da suka kai 12 za su tattauna a wannan taro ranar Alhamis a Abuja.

Kungiyoyin da suka shirya wannan taro sun hada ‘development Research & Project Center (dRPC)’ da ‘Partnership for Advocacy in Child and Family Health (PAS) project’.

Kungiyoyi sun shirya wannan taro ne domin tattauna matsalolin da kudirin ‘Task Shifting Task Sharing (TS) policy’ ke fama da su da hanyoyin da za a bi domin kauce musu wurin zantar da ayyukan da ya shafi fannin kiwon lafiya a kasar nan.

Bangarorin kiwon lafiya da Kudirin TS ke aiki a kai sun hada da inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana, cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro, tarin fuka da sauran cututtukan da ake kamawa ta hanyar shakar iska da sauran su.

Share.

game da Author