Wani a kan keke ya ta da bam a Maiduguri

0

Wani matashi daure da bam a kan keke ya kashe kan sa a Maiduguri.

Matashin ya ta da bam dinne a Unguwar Muna Datti a daren Litini.

Mutane uku ne suka mutu a harin, sannan wasu 17 sun jikkata.

Kakakin rundunar’yan sandan Jihar Joseph Kwaji ya tabbatar da aukuwar wannan hari sannan ya kara da cewa tuni an kai wadanda suka jikkata asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

Share.

game da Author