Za a koyar da unguwan zoma dabarun karbar haihuwa na zamani a Bayelsa

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Bayelsa Ebitimitulah Etebu yayi albishir cewa gwamnati za ta horar da unguwan zoma na gargajiya kan dabarun karban haihuwa ta zamani.

Ya fadi haka ne a taron tattauna aiyukkan da gwamnan jihar Seriake Dickson ya yi a jihar wanda ma’aikatar sadarwa ta shirya a Yenegoa ranar Talata.

Etebu ya ce horar da unguwan zoma kan dabarun karban haihuwa na zamani zai taimaka wa mutanen jihar samun ingantaciyyar kiwon lafiya kuma a saukake.

Daga karshe Etebu ya ce bayan horar da su da za ayi za kuma su shigar da su cikin tsarin N-power domin su amfana da aiki da gwamnati.

Share.

game da Author