Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya fadi cewa gwamnatin sa ta gama shiri tsaf don gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 200 a jihar.
Ya fadi haka ne bayan ya karbi sakamakon bincike da akayi kan matsayin cibiyoyin da ke sassan jihar.
Obaseki ya ce suna sa ran cewa za su kammala gyaran asibitoci 200 cikin watanni 24 amma za su fara da asibitoci 25 daga cikin su tsakanin nan da watan Afirilun 2018.