Shi ma Buhari ya bi sahun gwamnatocin baya wajen karya doka da sharuddan bada Kwangiloli

0

MATASHIYA:

Ita wannan doka an kafa ta ne domin tabbatar da cewa an bayar da kwangiloli a fili kuru-kuru bisa doka ba cikin nuku-nuku ko kumbiya-kumbiya ba.

Duk da cewa a lokacin kamfen a 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawurran nada mambobin Hukumar Kula Da Yadda Ake Bayar da Kwangilolin Gwamnatin Tarayya, NCPP,inda har yau ba a ayi ba.

Maimakon haka, sai Majalisar Zartaswa karkashin jagorancin shugaban kasa Buhari ta yi karfa-karfa, inda ta amshe mafi muhimmancin aikin hukumar, wato amincewa da ayyukan kwangiloli.

Tsohon Shugaban Kasa, marigayi Umaru ‘Yar’Adua ne ya sa wa dokar hannu a cikin 2007, a ranar 4 Ga Yuni domin kafa Hukumar ta NCPP da ta BPP mai sa ido kan ayyukan kwangiloli da bin yadda ake sayo kayan gudanar da dukkan ayyuka a ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnatin tarayya.

An kafa dokar ne domin a tabbatar ana yin abin a bisa ka’ida tare da shigo da jama’ar da abin ya shafa a ciki, ba tare da jami’an gwamnati su rika rufe daki su na yin tuwo-na-mai-na a batun raba kwangiloli ba.

Sai dai kuma shi kan sa ‘Yar’Adua da ya sa wa dokar hannu, bai samu damar kafa hukumar ba, ballantana har a yi aiki da ita. Shi ma Goodluck Ebele Jonathan da ya gaje shi, ya ki yin amfani da dokar a tsawon shekaru shida da ya yi a kan mulki.

Shi ma Buhari, sama da shekaru biyu kenan ya na mulki, amma tun da ya hau bai taba waiwayar kafa hukumar ba, duk kuwa da cewa a lokacin kamfen ya sa korafin rashin kafa hukumar, wadda ya yi alkawarun da ya hau zai kafa ta.

RA’AYOYIN ‘YAN NAJERIYA

Rashin kafa wannan hukuma da Buhari ya yi, abu ne da masana da kuma masu rajin yaki da cin hanci da rashawa ke ci gaba da yin tir da kuma caccaka.

Wasu da soki yadda Buhari da ministocin sa ke ci gaba da bayar da kwangiloli ba tare da kafa wannan hukuma ta NCPP ba, sun hada da tsohuwar Ministar Ilimi a zamanin mulkin Olusegun Ogasanjo, Oby Ezekwesili, da shugaban rajin kare hakkin jama’a da sa wa gwamnati idanu, CISLAC, Ahmed Rafsanjani da fitaccen lauyan nan na Lagos, Mista Effuong.

Rafsanjani ya ce, “ai babu abin takaici kamar yadda APC ta rika Allah-wadai da gwamnatin Jonathan, saboda ba ta kafa hukumar NCPP ba domin ta ji dadin daka wa dukiyar al’umma warwaso. Amma ga APC ta kafa gwamnati a karkashin Buhari, maimakon ta yaki cin hanci da rashawa, sai shi ma Buharin ya bi turbar Jonathan.

Ezekwesili ta ce ba karamin ganganci ake yi da haramci ba, wajen kin kafa hukumar NCPP da gwamnatin APC ta yi. Wannan kuwa inji ta, gwamnatin yanzu da wadda ta gada sun zama ” Tukura da Bako, wadanda duk Umbutawa ne”, tushen su daya.

Shi ma Effiong cewa ya yi, “ai duk wani wanda ya aiwatar da wani hurumin da hukumar NCPP ke da ikon gudanar da shi, to ya aikata haramtaccen abu, kuma aikata hakan babban laifi ne ainun.”

“Ba zai yiwu kasar nan ta tafi a kan wannan karkatacciya, baudadda kuma gurbatacciyar turba ba, ana yin mulkin danniya da karfa-karfa a cikin rigar dimokradiyya.” Inji Effiong.

Idan za a iya tunawa, lokacin da,Buhari ke kamfen ya yi alkawarin ba zai yi irin shirmen da Jonathan ya rika yi wajen bayar da kwangiloli gaba-gadi ba tare da kafa NCPP ba.

To ga shi an kusa shiga 2018, amma shiru ka ke ji, babu amo, kuma babu labarin kafa hukumar.

PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, wanda ya ce gwamnati na nan na kokarin kaddamar da wannan hukuma ba da dadewa ba.

Share.

game da Author