CUTAR SHAN INNA: Kasar Jamus ta tallafawa Najeriya da miliyoyin kudi

0

Jami’in kula da harka da jama’a na hukumar kiwon lafiya na matakin farko NPHCDA Sa’adu Salahu ya ce kasar Jamus ta tallafawa fannin kiwon lafiyar Najeriya da Ero miliyan 30 domin kawar da cutar shan inna a kasar.

Ya ce Najeriya ta karbi wannan tallafi ne a bukin rattaba hannu da tayi a takardun amincewa da yarjejeniyar hakan tsakaninta da kasar Jamus a Abuja, a makon da ya gabata.

‘‘Wadanda suka saka hannu a wannan takardan yarjejeniyyar sun hada da Regine Hess wakiliyar kasar Jamus,ministan aiyukkan waje Geoffrey Onyeama da shugaban hukumar kula da kiwon lafiya na matakin farko Faisal Shuaib.”

” Wannan itace tallafi na 9 da kasar Jamus ke ba Najeriya domin kawar da cutar shan inna a kasar.”

Bayan haka Geoffrey Onyeama tare da Faisal Shuaib a nasu tsokacin sun mika godiyar su na musamman ga kasar Jamus, WHO da UNICEF da sauran kungiyoyin bada tallafi don taimakon da suke yi wa fannin kiwon lafiyar kasar nan sannan sun kuma ce gwamnati na iya kokarinta wajen samar da isassun kudade domin ganin cewa ta kawar da cutar shan inna a kasarnan baki daya.

Share.

game da Author