PDP ta ce ta na nan daram

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa har yanzu ta nan kan ta a hade yake. Ta yi wannan bayanin ne jim kadan bayan da wasu masu ikirarin mambobin ta ne su ka bayyana kafa wata sabuwar jam’iyyar PDP, har suka bude ofis a Abuja.

Wadansu mutane biyar ne, su ka fito suka bayyana kafa wa jam’iyyar reshe, mai suna ‘Fresh PDP a ranar Laraba, a Abuja inda suka kaddamar da hedikwatar ofishin a cikin unguwar Asokoro.

Mutanen biyar sun hada da Franklyn Edede, Hassan Adamu, Obi Nwosu, Olusola Akindele da kuma Godwin Duru.

Idan ba a manta ba, irin haka ne aka yi wa jam’iyyar a cikin 2013, inda wasu gwamnoni suka balle, abin da ya yi sanadiyyar jam’iyyar ta fadi zaben 2015, inda ta sha kaye a hannun APC.

Edede da Duru sun yi takarar shugaban matasa na jam’iyyar PDP da kuma sakataren shirye-shirye,a zaben da jam’iyyar ta gudanar makonni biyu da suka gabata a gangamin da jam’iyyar ta gudanar a Abuja, amma ba su samu nasara ba.

Bayan an kayar da su, sai suka nemi hadin kan sauran wasu masu korafi, da kuma wadanda ke ta-ciki-na-ciki da zaben, suka nemi a soke zaben gaba daya, har shi kan sa na shugaban jam’iyya, wanda Uche Secondus ya yi nasara.

’YAN WASAN KWAIKWAYO NE, inji PDP

Kakakin yada labaran jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya yi watsi da mutane biyar din da aka ruwaito sun balle sun kafa reshen PDP, a matsayin ‘yan hauragiya kawai da kuma wasan kwaikwayo.

Ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa PDP ta na nan daram, kuma ba ta yi ko gezau ba, ballantana razana da jin labarin wasu gngun wadanda suka fadi zabe sun yi tsallen-badake su kafa wani reshe, ko wata jam’iyya can daban ba.

“Amma mu dama ai tuni mun san akwai jam’iyyar da ta rika yin fadi-tashin ganin ta yi wa PDP tadiya tun kafin gangamin jam’iyyar a Abuja”

“To duk cikin su in banda Fraklyn Edede, wane ne ya tsaya takara, kuma wane ne maid an dama-dama- sauran bas u ma kai karan-kada-miya ba cikin PDP ba.” Inji Kola.

Ya ci gaba da cewa shugabannin jam’iyyar PDP kan su a hade ya ke, kuma tun bayan zaben shugabann nin, jam’iyyar ta ci gaba da gudanar da harkokin ta ba tare da wasu matsalolin da za a iya cewa cikas ne ba.

Share.

game da Author