Kamfanin Dangote Group ya zargi BUA Group da aikin hakar ma’adinai a kadadar ma’adunai mai albarka, mai lamba No. 2541, da ke kan iyakar Oguda da Ubo, a yankin Okene, cikin jihar Kogi.
Wannan fangamemen wurin hakar ma’adinai dai ya haddasa rikici tsakanin manyan kamfanonin biyu da kuma Gidan Sarautar Omadivi na Okene, jihar Kogi.
Dukkan kamfanonin biyu dai su na ikirari har a gaban kotu da kuma wasikar da aka tura wa Shugaba Muhammadu Buhari korafi, cewa su ne aka bai wa lasisin hakar ma’adinai a wurin.
Ma’aikatar Ma’adinai da Karafa ta Tarayya ita ce ke da alhakin bayar da iznin amincewa kamfani ya haki ma’adinai a ko’ina cikin kasar nan.
Sakamakon kukan da BUA ya tura ofishin Shugaban Kasa, a ranar 4 Ga Disamba, 2017, Dangote Group ya amince a warware rikicin a bisa ka’idar da dokar kasa ta shimfida a cikin kundin dokokin kasar nan.
HUJJOJIN KAMFANIN BUA
Shi dai Shugaban Kamfanin BUA, Abduksamad Isyaka Rabi’u, ya rubuta wa Shugaba Buhari wasika a ranar 4 Ga Disamba, dangane da kiki-kakar da ke tsakanin Kamfanin sa da na Dangote.
Korafin wanda jaridu da dama sun buga shi, ya zargi Ministan Ma’adinai da yi wa BUA kafar-ungulu ta hanyar mara wa Dangote Group baya a kan rikicin.
Ya zargi Minista Kayode Fayemi da yin karfa-karfar kwace masa lasisin hakar ma’adinai mai lamba 18912 da kuma 18913 wanda su ke hakar ma’adinai a Obu-Okpella cikin Karamar Hukumar Etsako da ke jihar Edo.
Rabi’u ya jajirce cewa Kamfanin sa ne ke da hakkin hakar ma’adinai a wurin, domin a cewar sa, tun a ranar 17 Ga Yuni, 1998 aka ba shi lasisi.
HUJJOJIN KAMFANIN DANGOTE
Kamfanin Dangote ya ce ya sayi lasisin hakar ma’adinai a wurin daga hannun AICO Ado Ibrahim Company Limited a cikin 2014.
Dangote ya ce hujjoji da dama sun tabbatar da cewa Ma’aikatar Ma’adinai ta Tarayya ce ta bai wa AICO lasisin wanda Dangote ya saya a hannun kamfanin.
Dangote ya kawo hujjoji masu dauke da lambobin lasisi da dama.
Yayin da Hukumar Kula da Ma’adinai ta Kasa ta tabbatar da bai wa AICO lasisin hakar ma’adinai, kamar yadda Dangote ya tabbar, shi kuma gidan sarautar Atta Omadivi sun zargi Ma’aikatar Kula da Ma’adinai ta kasa da nuna bangaranci su na goyon bayan Dangote.
Duk da cewa dai rigimar na kotu, a gefe daya kuma an gabatar da korafin nuna son kai ga BUA Company.