WANI SALON HARAJI: Za a fara cin direbobi tarar N100,000 – FRSC

0

Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra, FRSC, Boboye Oyeyemi, ya bayyana cewa ana nan ana tsara yadda za a rinka tilasta wa duk wanda ya karya dokar tuki ya biya tarar naira dubu dari cur.

Oyeyemi ya bayyana haka, a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ranar Laraba a Abuja.

“Idan ka kama direba ya na waya a lokacin da ya ke tuki, to ai tarar naira N4,000 kacal ta yi kadan. Gobe ma sake yi zai yi, saboda ya na ganin naira 4,000 ba komai ba ce.

“Dama ana cin mai laifi tara ne, domin ta zama gargadi gare shi da kuma ishara don kada ya sake aikata laifin da ya aikata. Shi ya sa na ce ni ina goyon bayan majalisar tarayya da ta ke kokarin nan ba da dadewa ba, ta gyara doka, yadda za a kara tsawwala kudin tarar da za a rika cin direban da ya karya dokar tuki.

“Lokaci ya yi da za a fara cin direbobi tara da ta kama daga naira dubu hamsin (N50,000) zuwa naira dubu dari (100,000) a kowane laifi guda daya.” Inji Oyeyemi.

“ Ku dubi Lagos ku gani mana. A can ba a cin direba tara kasa da naira dubu hamsin (50,000), shi ya sa kowa ya shiga taitayin sa a garin.

“Duk da hukuma ta ba hukumar tara kudin haraji ba ce, amma dai ina goyon bayan tsawwalawar da za a yi. Domin haka zaka ga direba ya zo ya karya dokar fitilar kan titi. Saboda sun raina mu, za ka ji ma wani ya ce mana. “ba dai tarar naira N4,000 ba ce, sai me?”

Share.

game da Author