Finafinai da dama sun fito a 2017 sai dai da yawa daga cikin su basu shigo kasuwa ba. Wasun su da yawa suna sinema ba su fito ba tukuna.
A cikin finafinan da suka fito kasuwa kuma aka kalle su da yawa sun yi zarra.
Hassana Dalhat, da take yin sharhi akan finafinan Kannywood ta taya PREMIUM TIMES duba irin wadannan finafinai domin zabo biyar da suka burge a wannan shekara ta 2017.
5 – Kanwar Dubarudu – Wannan shiri na Barkwanci yayi matukar burgewa a 2017.
Ali Nuhu da ba a saba ganin sa a shiri irin na barkwanci ba ya taka rawar gani matuka a wannan fim.
Itama Rahama Sadau ta yi matukar nuna bajintar ta a fim din.
Masu kallo sun yaba wa fim din ‘Kanwar Dubarudu’ matuka domin ko an sha dariya.
4 – Auren Manga – Auren Manga shiri ne mai matukar ban dariya.
Shirin Auren Manga ya fito da jarumai kamar su Adam Zango a matsayin Figo, da Falalu Dorayi a matsayin Manga. Jaruma Hadiza Gabon ta taka rawar gani kwarai da gaske a shirin inda ta fito a matsayin matar Manga.
Shirin dai ya kayatar.
3 – Mansoor – Ko shakka babu cewa Fim din Mansoor ya manne a bakunan duk wani ma’abucin finafinan Hausa a shekarar 2017.
Jarumi Ali Nuhu,Maryam Yahaya, Sadiq Sani na daga cikin wadanda suka shana a wannan fim. Mansoor ya burge ‘yan kallo a 2017.
2 – Rariya – Tun kafin fitowar fim din Rariya, sunan ta cika gari fam. Ko ina ka bi Rariya, duk wanda ka gani yana zancen fim, zai ce maka Rariya, Rariya dai.
Wani abu da ya dada sa fim din yayi matukar suna shine wakar da akayi a fim din. Wannan waka ta samu karbuwa sosan gaske a Arewacin Najeriya. Matasa da ‘yan mata sun nuna hazakar su wajen gwada rawar.
Har wa yau Ali Nuhu ne da Rahama Sadau suka shana a fim din.
1 – Mijin Yarinya – Idan har za ka ba da labarin a kannywood wannan shekarar dole ka fidda fim din Mijin Yarinya ka sa shi a sahun farko.
Mafi yawan wadanda suka tattauna da PREMIUM TIMES sun tabbatar mana da cewa duk wani abu da kake so ka sani da ya shafi rikicin gidan mai mata, wannan shiri ya kun sa. Munafincin kishiyoyi ne, mulkin Amarya ne, rudewar mai gida ne, biyayya ga matan mahaifi da dai sauran su.
Sabuwar jaruma, Maryam Yahaya ce ta baza hazakar ta a fim din. Ta shana kuma ta dana. Idan baka gane ba ka tambayi Momo.
Wasu finafinai kamar su, Ciki da Raino, Kalan Dangi, Burin Fatima da suran su duk sun shana.