An sace Dan Majalisar Jihar Taraba

0

Masu garkuwa sun yi awon gaba da wani Dan Majalisa dake wakiltan Takum 1 a majalisar dokokin jihar Taraba jiya.

Rundunar ‘yan sandan jihar sun tabbatar da haka inda kakakin rundunar David Misal ya ce an sace Hosea Ibi ne a garin Takum a yayin da ya zo ziyara gidan mahaifiyar sa.

Masu garkuwan sun zo gidan Hosea ne da karfe 10 na dare inda suka amshe wayoyin duk Wanda suka ci Karo da shi a gidan sannan suka waske da shi Hosea.

Share.

game da Author