An kama wani makiyayi da laifi yi wa matan aure fyade a gonarta

0

Kotun karan dake garin Iyaganku a Ibadan jihar Oyo ta daure wani makiyayi da akae wa zargi ya yi wa wata matan aure fyade.

Alkalin kotun Patricia Adetuyibi ta ce Abubakar Likita dan shekara 19 ya yi wa wata matan aure fiyade a lokacin da ta ke aiki a gonarta ranar 14 ga watan Agusta da misalin karfe biyar na yamma a kauyen Ile-Ido kusa da kauyen Idiya jihar Oyo.

Ta ce sakamakon hakan matan ta sami rauni a goshinta domin sai da suka kaure da kokawa da abin ya fi karfinta sai ta mika wuya kawai inda shi kuma gogan naka ya baza bujen sa.

Patricia Adetuyibi ta kotu za ta ci gaba da ajiye makiyayin a kurkukun Agodi har sai ta ji daga babban kotu.

Share.

game da Author