Kotu ta yi barazanar daure Shugaban jam’iyyar APC Oyegun da sakataren sa

0

Babbar Kotun jihar Ebonyi, ta yi barazanar daure shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Odigie-Oyegun da sakataren sa, Mai Mala Buni saboda kin bin umarnin kotu.

Alkalin kotun H. A. Njoku ne yay i wannan barazabar inda y ace su biyun tilas su gabatar da kan su a gaban sa a ranar 28 Ga Sartumba, 2017, Domin su bayar da gamsasshen dalilin da ya sa ba zai daure sub a, dangane da take umarnin kotu da suka yi a rikita-rikitar shugabancin jam’iyyar a jigar Ebonyi.

Ran kotun y abaci ne saboda shugaban da sakatare sun ki bin umarnin kotu, bayan kotu ta haramta musu yin wani canje-canje a cikin shugabannin zartaswar jam’iyyar na jihar Ebonyi.

Rikici a jam’iyyar APC reshen Ebonyi ya barke ne bayan da Oyegun ya aika wa mataimakin shugaban jam’iyyar na jiha, Eze Nwachukwu wasika cewa an daga likkafar sa zuwa mukamin shugaba.

Ganin haka, nan da nan sai shugaban jam’iyyar na jiha wanda aka dakatar, Ben Nwobasi, ya bayyana cewa shi bai yarda an dakatar da shi ba, kuma sabon shigaban da aka nada, haramtaccen shugaba ne.

Wannan sa-toka-sa-katsi dai ta samo asali ne tun cikin 2014.

Share.

game da Author