Shugaban Hukumar Kula Da Aikin Hajji ta Kasa, Abdullahi Muhammed, ya umarci hukumomin aikin Hajji na jihohi da su kara wa’adin karbar cikon kudade daga hannun maniyyata zuwa nan da sati daya.
Shugaban ya bada wannan umarni ne a filin jirgin Abuja a yayin da ya ke sa hannun yarjejeniya da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar maniyyatan na 2017.
Ya ce karin wa’adin sati daya ya zama tilas domin a kara bayar da dama ga dukkan maniyyatan da ba su cika kudin su ba, su samu su cika. “Aikin Hajji umarni ne kuma idaba ce, don haka a na mu bangaren ya zama wajibi mu tabbatar da cewa mutane sun samu saukin samun damar cika sauran kudin da ba su karasa cikawa ba.”
Shugaban ya kuma jaddada yakinin da ya ke da shi cewa dukkan kamfanonin sufurin jiragen da za su yi jigilar maniyyata da kuma dawo da mahajjata gida, duk nagari ne, ba za su ba Najeriya kunya ba.
Daga nan sai ya yi kira ga jiragen sufurin da su hada kai a tsakanin su wajen yi wa kasar nan hidima a lokacin jigilar ta wannan shekara.
Da yake magana a madadin sauran kamfanonin sufurin jiragen, shugaban Medview Munir Bankole, ya gode wa hukumar dangane da kwarin guiwar da ta ce ta na da yakini a kan jiragen, sannan ya tabbatar da cewa ba za su ba Nijeriya kunya ba.
Kamfanonin sufurin jiragen da za su yi jigilar maniyyata a bana, sun hada da Medview Airlines, Max Air da kuma Azman Air, wanda shi a wannan shekarar ne zai fara jigilar maniyyata a karon faron farko.
Ana sa ran wani kanfanin jirgin kasar Saudiyya wanda shi ne cikon na udu, zai rattaba hannu a yarjejeniyar a cikin wannan satin.
Discussion about this post