Mazaunan kauyen Federe Angwari sun yi zaman dole a gidajen su sanadiyyar ruwan sama da a ka sheka kamar da bakin kwarya in da ya karya wata gada da ke hada kauyen da wasu garuruwa da ke yankin.
Kauyen Federe Angwari na karamar hukumar Jos ta Gabas ne , Jihar Filato.
Da ya ke zantawa da manema labarai, wakilin Al’ummar Federe, Agwon Izere Isaac Wakili ya ce sanadiyyar wannan ruwa da a aka tafka a kauyen, Manoma, Yan kasuwa, yan makaranta da ma’aikatan gwamnati duk sun gagara fito zuwa wajen sana’arsu.
“Mutane sun kasa shiga cikin garin Jos domin gadan Federe Angwari ta karye.”
“Duk ranar da aka yi ruwan sama yaran mu basa iya zuwa makaranta don kusan kullum ana sheka ruwane inda akan kai har tsawon makonni biyu ruwan na sauka.”
“Saboda hakan muke kira ga gwamanti da ta kawo mana daukin gyara mana wannan gada”.
Dan majalisar wakilai dake wakiltan wannan yanki Joshua Madaki ya ce ya sanar wa majalisar jiha halin da mutanen yankin suka shiga.
Ya ce duk da cewa babu wanda ya mutu amma mutanen yankin sun rasa dukiyoyinsu wanda ya hada da gidaje, gonakai, dabobi da sauransu.