Hukumar kiddiga ta kasa NBS ta sanar da cewa farashin doya a kasuwanni ya tashin gwauron zabi tun bayan sanar da fara safarar sa zuwa kasashen waje.
Bayanan da hukumar ta bayar na watan Yuni 2017 mai taken ‘kula da farashin wasu abinci’ ya nuna cewa farashin kudin kilo daya na doya ya karu da kashi 32.84 bisa 100 tsakanin watan Yuni 2016 zuwa Yuni 2017.
Ministan aiyukkan noma Audu Ogbeh da yake kadamar da fara fitar da doya zuwa kasashen waje ya ce hakan zai taimaka wajen samar da aiki ga matasan kasar sannan ya rage yawan dogaro da a ke yi da man fetir.
Audu Ogbeh ya ce Najeriya na noma kashi 61 bisa 100 na doya a kasar sannan kuma mutanen kasa ba za su iya cinye doyar ba wanda hakan ya zama dole a fitar da shi zuwa kasashen waje domin guje wa hasarar doyar da kuma samar da wata hanya na samun kudaden shiga.
A haka ne kuma rahotanni daga musamman wasu sassa na kasar nan ya nuna cewa ana samu hawhawar farashin abinci da yafi Kamari a yankin arewa maso gabashin kasar.
Duk da cewa mutane suna fama da tsadar abinci a kasar bincike ya nuna cewa an samu faduwar farashin wasu kayayyakin abinci a watan Mayun da ya gabata.