Hukumar NDLEA ta kona wasu miyagun kwayoyi a Abuja

0

Hukumar tace ta yi haka ne don bin Umarnin wata kotu a Abuja.

Alkalan kotun Nnamdi Dimgba da A. Abdulkafaratisu sun yardar wa hukumar ta kona wadannan mia kwayoyi da ta kama a lokacin da ta ke yanke hukunci akan hakan.

Kwayoyin da aka kona ya kai kilo 24,304 a kudi Naira miliyan 250.

Shugaban hukumar NDLEA Muhammad Abdullah ya ce hakan shine ya fi dacewa da hukumar da kuma kasa baki daya domin barinsu zai iya haifar da mummunar matsala a kasar.

Bayan haka ministan Abuja Muhammed Bello a lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa a taron kona wannan miyagun kwayoyin ya jinjinawa hukumar NDLEA kan kokarin da take yi wajen kawar da miyagun kwayoyi a kasar sannan kuma ya yi kira da su ci gaba da yakin da suke yi a tashoshin motoci da kauyukan kasarnan.

Sarkin Abaji kuma shugaban sarakan gargajiya na Abuja Adamu Yunusa ya yi kira ga matasan su guji shan miyagun kwayoyi.

Shugaban hukumar NDLEA na Abuja Obijuru Chinyere tace hukumar za ta zafafa yakin da take ba hana amfani da miyagun kwayoyi sannan kuma za ta hada karfi da karfe da malaman makarantu,malaman addini, shugabanin unguwanni don ganin an kawo karshen wannan matsalar.

Share.

game da Author