Gwamnatin Kaduna ta kori ma’aikatan KASTELEA 124

1

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori ma’aikatan Kula da bin dokar hanyoyi da gyara muhalli 124 saboda saba wasu dokoki da ya hada da karban cin hanci wajen masu laifi da sauransu.

Kamar yadda shugaban hukumar KASTELEA AbdulKadir Ahmed ya sanar ya ce hukumar ta sallami mutum daya saboda kama shi da ta yi dumu dumu yana karban cin hanci. Sauran kuma suna gujewa wajen aikinsu.

Share.

game da Author