Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa, NULGE, ya bayyana a cikin takaici cewa a yanzu haka jihohi kimanin 23 ne suka kasa biyan ma’aikatan Kananan Hukumomi albashin su.
Da ya ke magana da kamfanin dillancin labarai ranar Litinin a Abuja, shugaban ya ce akwai jihohin da ake bi albashin watanni daya, wasu biyu, akwai kuma har wadanda ake bi watanni 16.
Ya ce abin takaici ne jihohi kamar Bayelsa ana bin ta wata goma zuwa 16 na kudaden ariyas. Sai Kogi watanni bakwai zuwa 15 da kuma Delta da ake bi watanni takwas zuwa 14.
Sauran jihohi sun hada da Kaduna wata 12; Oyo wata 11: Edo wata 10; Abia wata biyar zuwa tara. Sai kuma Kwara da Binuwai wata tara su ma.
Khaleel ya ce akwai jihohi irin su Ondo, Ekiti da Imo da ake bi albashin watanni shida sai kuma Zamfara wadda ba ta ma fara yin amfani da tsarin albashi mafi kankata da aka amince da shi ba.
Ya kuma yi jimamin yadda jihar Enugu ke biyar rabin albashi har tsawon watanni 24. Daga nan ya yi kira ha gwamnoni da cewa kada su taba kudin tallafin da gwamnatin tarayya ta ba su daga lamunin Paris Club, ba tare da ta fara magance matsalar albashin ma’aikata ba.
Ya kuma jinjina wa jihohin Lagos, Ogun, Kano, Katsina, Jigawa, Sokto, Kebbi, Barno, Bauchi, Gobe, Gombe, River, Neja da Anambara wadanda ya ce ba su yin wasa da hakkin ma’aikatan kananan hukumomin su.
Ya kuma nuni da cewa rashin biyan hakkokin ma’aikata na tsunduma su cikin halin kunci da tagayyara. Sai ya yi kira ga gwamnoni da su guji tura ma’aikatan kananan hukumomi a cikin halin kaka-ni-ka-ka-yi.