Wata harkallar da aka bankado ta dabaibaye hukumar ‘yan sandan leken asiri na farin kaya, SSS, inda aka gano son kai da nuna bangaranci wajen daukar ma’aikatan da aka yi a hukumar, wadanda suka kammalla karbar hoto kwanan baya a jihar Legas.
Hukumar dai ta kaddamar da jami’ai 479 da ta dauka, wadanda ta yaye a Legas ranar 5 Ga Maris, 2017. An yaye su ne bayan sun samu horo a fannin dakile harin sari-ka-noke, leken asiri, binciko bayanai, koyon sarrafa bindigogi da horo na motsa jiki.
Sunayen jami’an tsaron wanda Premium Times ta samu, ya nuna irin yadda ba a yi raba-daidai ba tsakanin jihohin kasar nan 36 da Babban Birnin Tarayya, a wajen daukar ma’aikatan.
A bisa ka’ida, kowace jihar an ce jami’an tsaro 5 kacal za a dauka, duk wadanda suka cika fam na neman aikin an sa sun zauna wata jarabawa a jihohin su na asali. An kuma dauki jami’ai biyar daga kowace jihar, kamar yadda aka shar’anta.
Sai dai kuma wasu abubuwan da suka biyo baya sun tabbatar da cewa akwai harkalla sosai a cikin tsarin da aka bi aka yi wa wasu jihohi aringizo, yayin da wasu kuwa aka yi musu kwange.
An yi wa Jihar Katsina, jihar Shugaban Kasa da kuma shi kan sa shugaban hukumar SSS, Lawal Daura, aringizon daukar jami’an tsaro har 51, Akwa Ibom kuma 5 kacal. Har yanzu dai ba a san irin tsarin da hukumar ta bi ta yi irin wannan tsarin daukar jami’an tsaron ba.
An dauki mutum 25 daga Kano, yayin da aka dauki 7 kacal daga jihar Legas. Za a iya lura da cewa an dauki 165 daga shiyyar Arewa-maso-yamma, yayin da Kudu-maso-yamma aka dauki 51 kawai. Ga dai yadda lissafi da adadin wadanda aka dauka nan daga kowace jiha da kuma Babbann Birnin Tarauyya.
Har yanzu dai Premium Times ba ta ji bayani daga hukumar ba, na yadda aka yi wannan harkallar daukar jami’an tsaro. An buga wayar Lawal Daura, shugaban humumar, amma har zuwa yanzu bai dauka ba, kuma bai kira ba.
Shi ma shugaban hukumar daukar ma’aikata ta kasa, Shettima Bukar Abba, an kira shi domin a ji ta bakin sa, kasancewa hukumar sa c eke da alhakin daukar ma’aitaka.