Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta taba tsallake siradin matsalar tattali arziki da wahalhalun zamantakewar al’umma ba, har sai an sake tsarin Federaliyya da ake tafiyar da gwamnati akai yanzu.
Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke gabatar da wata takarda wadda ta shafi kalubalen zaman tare a tsakanin al’ummomin kasar nan a karkashin gwamnatin tarayya. Ya yi jawabin ne a taron kaddamar da jaridar Daily Stream, a dakin taro na Cibiyar Gudanar da Tarurruka ta Sojojin Saman Kasar nan, a Kado, Abuja.
Ya ce ya na nan a kan bakan sa cewa tsarin da muke a kai, wanda sai dai duk wata a rika kasafta dukiyar kasa, ba tare da maida hankali wajen abin da kowace jiha ke amfanawa ko za ta iya amfanawa ba, babbar matsala ce mai zaman kanta.
Ya yi tsokaci da cewa har yau duk lokacin da aka yi kididdigar ma’aunin ci gaba, Najeriya a sahun bayan sauran kasashen da ya kamata a ce mun yi musu fintinkau ta ke. Amma har yau, “ba mu da bayanin komai daga fatara, talauci, yunwa, tsadar rayuwa da tsadar abinci, rashin aikin yi, tsadar kudaden kasashen waje, yawan mutuwar jirajirai da mata masu juna biyu a wurin haihuwa, jahilci da kuma tulin yara masu gagaramba a gari ba karatu.”
“Matsawar ba mu gyara tsarin siyasa, tsarin gwamnati da tsarin tattalin arzikin mu ba, to ba za mu iya matsawa ko daga nan zuwa can ba, da sunan ci gaba.” Inji Turakin Adamawa.