Hukumar kula da jindadin mahajjatan jihar Taraba ta sanar da cewa sama da kashi 90 na maniyyata aiki hajjin bana daga jihar Taraba manoma ne.
Babban sakataren hukumar Umar Leme ya ce manoma sun biya sama da naira miliyan 900 ga hukumar kafin gwamnati ta fadi ainihin kudin aikin hajji na bana.
Leme ya ce hakan yana da nasaba ne da irin dimbin amfanin gona da manoma suka samu a damunan bara.
“ Hukumar ta kama wa maniyyatan jihar gidaje kusa da harami sannan gwamnatin tarayya ta ba jihar kujeru 1, 457 amma jihar na kokarin ganin an dan kara mata kafin lokacin tafiya.”