Tsohon gwamnan jihar Zamfara Mahmuda Aliyu Shinkafi ya canza sheka zuwa jam’iyyar APC.
Mahmuda ne dan takaran gwamnan jihar a jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata.
Ya sanar da canza shekar nasa ne yau a garin Gusau inda ya yi kira ga magoya bayansa da su bishi zuwa jam’iyyar APC din.
Ya Kara da cewa yayi hakanne domin ya bada nasa gudunmawar a jihar.
Mahmuda Shinkafi ne mataimaki Ahmed Yerima a lokacin da yake gwamnan jihar.