Wasu dauke da bindiga sun kashe wasu fulani makiyaya biyu a kauyen Unguwan Yashi dake kudancin jihar Kaduna.
Shugaban Miyetti Allah na jihar Ibrahim Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar hakan.
Yace Anas Shu’aibu mai shekara 20 da Yahaya Musa dan shekara 14 sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kiwo a kauyen Anguwan Yashi dake karamar hukumar Jema’a.
Ibrahim Abdullahi ya roki fulani makiyaya da suyi hakuri da wannan kisa cewa jami’an tsaro za su bi ma wadanda aka kashe hakkinsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Kaduna Aliyu Uthman ya tabbatar da harin sannan ya ce an kama mutane 9 a dalilin hakan.