An sake tsinto gawar wani fulani makiyayi a kauyen Madakiya, Zango Kataf

0

Awoyi bayan sanar da kashe wadansu makiyaya biyu a Anguwan Yashi dake karamar hukumar Jema’a, kudancin Kaduna an sake tsinto gawan wani makiyayi a kauyen Madakiya dake karamar hukumar Zangon Kataf.

Shugaban kungiyar fulani makiyaya na Miyetti Allah Ibrahim Abdullahi a madadin kungiyar na kasa ya ce abinda akayi wa ‘yan uwansu bai dace ba.

Kungiyar ta yi kira ga fulani makiyaya da suke yankin da suyi hakuri su zauna lafiya domin gwamnati da jami’an tsaron jihar na kokarin ganin an kama wadanda suka aikata wannan aiki.

Wasu dauke da bindiga sun kashe wasu fulani makiyaya biyu a kauyen Anguwan Yashi dake kudancin jihar Kaduna.

Shugaban Miyetti Allah na jihar Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da faruwar hakan.

Yace Anas Shu’aibu mai shekara 20 da Yahaya Musa dan shekara 14 sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kiwo a kauyen Anguwan Yashi dake karamar hukumar Jema’a.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Kaduna Aliyu Uthman ya tabbatar da harin sannan ya ce an kama mutane 9 a dalilin hakan.

Share.

game da Author