Sarkin Kano Muhammadu Sanusi yayi kira ga gwamnonin Arewa da su mai da wadansu masallatansu makarantu.
Sarkin Kano ya fadi hakanne a bukin makon ilimi da aka yi a jihar Kano.
Sarki Sanusi yace mai da masallatai makarantu zai rage kudaden da gwamnati take kashewa wajen gina sababbin makarantu da wadatar dasu da kayayyakin aiki.
Yace a zamanin da masallatai ne makarantu da kotu na, saboda haka ya shawarci gwamnonin da masallatai suka yi yawa jihohinsu da su mai da wadansunsu makarantun firamari.