Yau ne aka yi bukin sunar ‘yar shahararren mawaki kuma jarumi a wasan fina-finan Hausa Adam Zango a garin Kaduna.
Amaryan Adam Zango, Ummul Kulsum ne, ta haifa wa jarumin ‘yar sa ta mace ta farko acikin jerin ‘ya’yansa wanda duk maza ne ranar Talatar da ta gabata.
Tun daga wannan rana ne Adam Zango yake ta sanar wa aminansa da abokanan aikinsa domin su taya shi murna akan hakan.
Adam Zango yace bai taba yin bukin suna ba amma zai yi bana saboda Allah ya bashi abun da yake ta nema wato ‘ya mace.
Ya gode wa Allah da irin zumunci da abokanai da masoya suka nuna masa da iyalansa a wannan rana.
Abokanan arziki da masoya ne suka ziyarci bukin sunan Murjanatu.
Kalli bidiyo anan