Kwamishanan ilimin jihar Zamfara Mukhtar Lugga ya ce wata cuta da ba’a gane ko wace irin cuta bace ta yi sanadiyyar rasuwar dalibai 3 a makarantar Arabi da ke garin Maradun.
Kwamishinan ya fadi hakan ne wa manema labarai ranar Laraba a Gusau.
Ya ce ranar Laraba jami’an makarantar suka kai dalibai 2 babbar asibitin dake Maradun.
Ya kuma ce bisa ga bayanan da hukumar makarantar ta bayar, an fara ganin alamun cutar ne akan wasu dalibai a makarantar tun daga ranar litinin da ya gabata.
A halin da ake ciki gwamnatin jihar Zamfara ta gaiyato kwarrarun likitoci domin su nemo hanyar da za’abi domin shawo kan barkewar wannan cuta da samarda magani ga wadnda suka kamu da cutar.
Bayan haka gwamnatin jihar ta ware wani sashe a asibitin makarantar domin killace wadanda suka kamu da cutar da kuma samar musu da kula da kuma yin hakan a babbar asibitin da ke Maradun.
Kwamisahina Mukhtar Lugga ya ce suna nan suna sauraron sakamakon gwaje-gwajen da likitocin za su fitar akan cutar kafin su san wani mataki gwamnati za ta dauka domin kawo karshenta.