Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce Gwamnatin Najeriya ta kardamar da sabuwar shiri domin bunkasa kiwon lafiya a kasa Najeriya.
Adebowale ya fadi hakan ne bayan zama ta mako mako da majalisar zantarwa ta yi a Abuja.
Ministan Adebowale yace dokar mai taken ‘’Bunkasa kiwon lafiyar mutanen kasa Najeriya domin samun ci gaba mai dorewa” itace ta uku da aka yi a tarihin Najeriya bayan wadanda akayi a shekarar 1988 da 2004.
Adebowale ya ce kafin gwamnati ta kirkiro dokar sai da ta kafa wata kwamiti da ya hada da tsohuwar ministan kiwon lafiya Farfesa Eyitayo Lambo wanda nauyin gyara matsalolin da fannin kiwon lafiya ke fama da shi ya rataya akan su.
Ya kuma ce dokar za ta taimaka wajen samun nasara akan burin gwamnati na bunkasawa da wadata fannin kiwon lafiya da duk irin abubuwan da take bukata domin musamman talakawan Najeriya.