Makwabtan gidan da Andrew Yakubu ya boye daloli suna cizon yatsa

0

Tsohon shugaban kamfanin mai na Kasa (NNPC) Andrew yakubu ya boye daloli da yakai sama da biliyan uku a wata gida nasa da yake unguwar Sabon Tasha dake Kaduna.

Gidan Jaridar Premium Times ta ziyarci unguwan domin tattaunawa da mazauna unguwan akan yadda suka ji da aka ga irin wadannan kudade a wannan gida.

Grace John, malaman makaranta ta ce wannan abu baiyi mata dadi ba.

“Maimakon barayin da ke yi mana sace sace a gidajen mu su bi irin wadannan gidaje sun bari irin wadannan makudan kudi na zama a unguwan ba’a sani ba sai namu kanana suke ta bi. Andrew Yakubu mugu ne na gasken gaske.”

Blessing Luka, mai siyar da lemon zaki a unguwar Sabon Tasha ta ce ta dade tana neman shi Andrew din ya bata jarin 10,000 amma abun ya gagara. “Ashe akwai sama da naira biliyan uku a cikin wata tsohuwar gidansa a nan unguwar.

Amma bai kyauta ba.”

Jacob Dominic Yace Allah ne ya tona masa asiri amma da ba bu wanda zai san menene ke faruwa a wannan gidan. “Ko da yake naji wai yana tara kudi domin ya na so ya yi takaran gwamnan jihar Kaduna a zabe mai zuwa.”

Wasu da yawa da suka tattauna da PREMIUM TIMES sun ce da sune suka sami irin wadannan kudade da sun taimakawa mutane da shi.

Share.

game da Author