Wata kotu a kasar Amurka, ta dakatar da dokar hana shiga Kasar da Shugaban kasar Donald Trump ya sanya wa hannu don haramtawa ‘yan kasashen Libya, Syria, Iran, Iraq, Sudan, Yemen da Somalia shiga kasar.
A sanadiyyar hukuncin da wannan kotu ta yanke hukumar shige da ficen kasar Amurka, ta yardan ma duk wani kamfanonin jiragen sama da yake jigalan matafiya daga wannan kasashe da su koma bakin aikinsu na dauko matafiya da ga wadannan kasashe.
Alkalin kotun da ya yanke wannan hukunci ya ce umurnin shugaban kasar Donald Trump ya sabawa tsarin mulkin kasar.
Ko da yake fadar gwamnatin Amurka din sun nuna rashin jin dadinsu akan hakan, sunce zasu kalubalanci wannan hukunci.
Rahotanni ya nuna cewa mafi yawan ‘yan kasashen da Trump ya hana shigowa kasar Amurka din dalibai ne da ma’aikata kuma sun fuskanci matsi daga hukumomin shiga da fitar kasar a ‘yan kwanakinnan.
Wannan hukunci dai yayi wa kashen duniya da yawa dadi wanda tun farko sun nuna rashin amincewarsu da haka.