Sanatoci 20 za su koma PDP

0

Tsohon gwamnan jihar AkwaIbom Sanata Godswill Akpabio y ace akalla sanatoci 20 suke shirin canza sheka zuwa jam’iyyar PDP da zaran jam’iyyar ta gama gyara gidanta.

Sanatan ya fadi hakanne a taron jam’iyyar da akayi a Abuja jiya.

Yace sanatocin suna jiran a daidai ta ne tsakanin bangaren Makarfi da na Ali Modu Sherrif.

Daga karshe yace mulki za ta dawo hannun jam’iyyar a 2019.

Share.

game da Author