Ya’yan Laftanar Kanar TJ Abdullahi biyu sun rasu a hadarin mota

0

Sojannan da ya ke tsare saboda kiran shugabannin sojojin Najeriya yan wasan kwaikwayo ya rasa ‘ya’yan sa biyu a wata hatsarin mota a hanyar su na dawo daga Maiduguri bayan ziyara da suka Kai wa ubansu dake daure.

Matarsa tana kwance a asibiti rai a hannun Allah.

Direban motar dake dauke da iyalan Abdullahi din shima ya rasa ransa.

Laftanar kanar TJ Abdullahi Wanda ba’asan inda rundunar sojin ta ke ajiye da shi ba na fuskantar horo ne saboda hira da yayi da abokanan aikinsa sojoji akan yadda manyan su ke wulakanta su da nuna musu halin ko in kula akan wahalar da sojonin ke fama dashi a dajin Sambisa wajen yaki da Boko Haram.

Kakakin rundunar Sojin SK Usman ya ce ba’a bashi damar yin magana akai ba.

Share.

game da Author