Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta ce za ta bude idanuwan ta sosai daga yanzu domin ganin ba’a ci mutuncin wani mabiya addinin Kirista ba akasarnan sannan ba a muzguna wa Faston Ikilisiyar Omega Fire Ministries, Johnson Suleman musamman ganin harin da jami’an tsaro suka kai masa a makon da ya wuce.
CAN din ta ce bata ga wani abinda zai sa a nemi kama Faston ba saboda kawai yace wai mabiyan sa su kashe duk wani Fulani makiyayi da suka gani ya zo kusa da cocin sa.
Kungiyar ta zargi mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da nuna halin ko in kula akan yadda Fulani makiyaya ke kashe mutane a yankin kudancin jihar Kaduna musamman kiristoci.
Da yake jawabi akan hakan Fasto Johnson Suleman ya ce ya fadi haka ne domin ya kare kansa daga harin da fulanin suke shirin kai masa duk da wai ba yana so ya kashe duka Fulani bane sai wadanda suka shigo harabar cocinsa.
Ya kuma zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa wai ya ki yin komai akan hakan.
Shugaban kungiyar CAN, Bayo Oladeji ya ce kamata ya yi jami’an tsaron su kira Faston domin su tuhumeshi ba kawai su je su nemi kamashi ba kamar wani mai laifi.
Yace kungiyar ba zata nade hannu ta bari ana muzguna ma mabiyanta ba da limamanta ba.
Daga karshe kungiyar ta yi kira ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo da yakwato hakin kiristocin kasa Najeriya domin mukamin da yake kai a yanzu hakan ya same ta ne saboda ya kare hakin su mabiya addinin kirista a kasa Najeriya.