Jaruma ‘yar wasan finafinan Hausa Jamila Umar Nagudu ta karyata rade-radin da ake ta yadawa wai Allah yayi mata rasuwa.
Jamila ta ce tana nan cikin koshin lafiya bata mutu ba kuma.
Ta fadi hakanne a wata sako na bidiyo da ta saka a shafinta na Instagram jiya Asabar.
A bidiyon Jamila ta ce a wannan lokacima za ta yi tafiya ne zuwa garin Kaduna daga Kano.
Tare da yan uwanta tana wasa da raha a tsakaninsu.