Gwamnatin Najeriya tace ba za ta iya canza ranar da shirya domin zuwa dajin Sambisa ba kamar yadda Kungiyar neman a dawo da ‘yan matan Chibok (BBOG) suke nema ba.
Ministan watsa labarai Lai Mohammed ya sanar wa kungiyar cewa gwamnati ba za ta iya canza ranar tafiyar ba saboda shirye-shiryen da ta riga ta gama akan hakan.
Gwamnati ta gaiyaci yan kungiyan da su zo suma a tafi dajin ranar litinin da su.
Ko da yake kungiyar BBOG din sun rubuta ma gwamnati wasika domin a daga tafiyar ministan yace tafiyar ya kunshi mutane ne da yawa wanda ya hada da jami’an tsaro na soji, kungiyoyi da ‘yan jarida in da kuma kowa ya gama shiri. Idan har za’a daga toh zai bukaci kashe wasu kudin bayan wanda aka riga aka kashe yanzu.
Gwamnati ta nemi kungiyar da ta bada akalla mutane 3 domin su bi tawagar da zasu shiga dajin Sambisa din domin gani ma idanuwarsu irin nasarorin da aka samu a yakin da akeyi da kungiyar Boko Haram da kuma neman ‘yan matan Chibok da aka sace.