Barayin Shanu sun dawo da dabbobi sama da 28,000 a jihar Katsina

0

Barayin shanu masu yawa ne suka tuba a garin Kankara da ke jihar Katsina.

Barayin da suka ajiye makamai sun mika bindigogi kirar AK 47 guda 104 da wadansu muggan makamai.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa ne ya kar be su a wata buki da aka shirya domin hakan a garin Kankara.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari a jawabinsa da sakataren gwamnatin jihar Mustapha ya karanta yace gwamnatin jihar ta roki barayinne da su yi hakuri da wannan sana’a nasu su zo gwamnati za ta laminta musu domin a samu zaman lafiya tsakaninsu da musamman manoman jihar da makiyaya.

Gwamnan yace za’a gina musu makarantu da asibitoci a kauyukansu.

An dawo da dabbobi sama da 28,000 inda aka maida wa masu shi abinsu.

Mutanen kauyukan da aka dawo musu da dabbobin nasu sun gode ma gwamnan jihar da irin kokarin da yakeyi domin ganin an sami zaman lafiya a jihar da kuma dawo musu da dukiyoyinsu da yayi.

Share.

game da Author