Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya amince da nadin Mohammed Tanko a matsayin sabon shugaban Jam’ian jihar Kaduna wato, KASU.
Mohammed Tanko dai shine mataimakin shugaban jami’an kafin nadin nasa.
Mohammed Tanko ya yi karatunsa a Jami’ar Bayero da ke Kano da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Ya fara aiki da jami’ar jihar Kaduna a shekara ta 2005.