Kwana ɗaya bayan Kotun CCT da ke Abuja ta dakatar da Muhuyi Magaji, Shugaban Hukumar Hana Cin Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), shi kuma ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara ya maka Hukumar CCB, wadda ke ƙarƙashin shugabancin Ɗanladi Umar.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito cewa alƙalai uku ne a ƙarƙashin Mai Shari’a Ɗanladi Umar, suka yanke hukuncin dakatar da Magaji a ranar Alhamis, bayan zargin sa da aka yi a gaban Hukumar CCB da laifin karɓar rashawa.
Danladi Umar ya ce CCT na da hurumin dakatar da Magaji. Don haka kotun ta umarci Gwamnan Jihar Kano da Sakataren Gwamnatin Kano su naɗa wani da ya cancanta ya riƙe hukumar kafin a kammala shari’ar tuhumar da ake wa Muhyi Magaji.
Ya ce Magaji ba zai iya ci gaba da riƙe Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano ba, a lokaci guda kuma ya na fuskantar tuhuma a kotu.
Yayin da Magaji bai gamsu da hukuncin CCT ba, sai ya umarci lauyan sa kuma Babban Lauya, Adeola Adedipe ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja.
A ƙasar da Muhyi ya shigar ranar Juma’a, 5 ga Afrilu, lauyan sa Adedipe ya bayar da dalilai biyar waɗanda ya kafa hujja da su cewa wajibin kotu ne ta yi adalci ta watsar da hukuncin dakatarwar da CCT ta yi wa Muhyi Magaji.
Ya bada hujjar cewa CCT ta tafka kuskure tare da ɗirka kwakyariyar rashin yi wa wanda yake karewa shari’a mai adalci.
Ya ce bai kamata a dakatar da Muhyi ba, tunda Shari’a aka fara, ba a same shi da laifi ba.
Saboda haka har yanzu Muhyi Magaji ba mai laifi ba ne, babu wani dalilin da zai sa a dakatar da shi daga muƙamin sa.
Lauya ya ce idan CCT ta ce Muhyi ya ajiye aiki kafin a kammala shari’a, ta ta yanke hukuncin cewa shi mai laifi ne kenan.
“Saboda haka hukuncin da su Ɗanladi Umar suka yi a Kotun CCT ba hukunci ba ne, ƙarfa-ƙarfa ce maras adalci ko kaɗan.”
Lauyan ya ƙara da cewa Kotun CCT ta tafka shirme, ta yadda ya bayar da umarni ga Gwamnan Kano Abba Yusuf da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, alhali su ba su ma cikin waɗanda ake ƙarar.
Lauya ya ce Kotun CCT ba ta da hurumin ba su wannan umarni na su naɗa wani shugaban riƙo a hukumar hana cin rashawa ta Jihar Kano.
Ya kuma ce Kotun CCT ta tafka kuskure da ta yi gaggawar cewa Magaji zai iya yi wa shari’ar da ake yi masa katsalandan, idan ya na kan muƙamin sa, alhali babu wata shaida ko alamar hujjar da ta nuna zai yi hakan.
Ya ce CCT ta yi gaggawar yanke hukuncin dakatar da Muhyi bisa amfani da ji-ta-ji-ta, maimakon ta tsaya ta kammala bincike tukunna.
Daga nan ya nemi Kotun Daukaka Ƙara ta jingine dakatarwar da CCT ta yi wa Magaji, har zuwa lokacin da ta yanke hukunci tukunna.
Discussion about this post