Shi tsarin J-Teach wani tsari ne da gwamnatin da ta gabata ta Gwamna Badaru ta bullo da shi, din cike gibin Malaman Makarantar da Jahar Jigawa ke fama da shi.
Ko da a baya, mun sha yin surutan cewa ko kadan wannan tsarin ba zai daure ba, kawai zai haifar da matsalar ne a gaba.
Ni tawa shawarar ma, Gwamnati ta soke wannan tsarin, ta maida hankali wajen daukan Malamai na din din din kamar yadda yadda yake a al’ada.
kamata duk wanda zai yi magana a kan wannan yanayin da a ka shiga na maida wannan malamai na din-din-din da yasan ma menene matsalar ilimin Jahar Jigawa, musamman ma na basic.
Kadan daga cikin matsalolin da Gwamna Danmodi ya gada.
Rashin Inganci Malamai (Teacher Quality).
Tun kafin zuwan gwamnatin baya ma a 2015, bincike ya nuna, a cikin matsalolin da suka baibaye, rashin Inganci ilimi a Jahohi da dama na Nijeriya, har da Jahar Jigawa a ciki, shine rashin ingantattun malamai.
Bincike ya nuna, Yara kan gama Makarantar primary ma, basa iya yin rubutu, karatu da karamin lissafi. Wannan ya sanya wasu Jahohin suka dauki matakan gaggawa dan kawo karshen matsalar.
Misali, za a iya tuna danbarwar tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Elrufa’i, da yayiwa dukkanin malaman Jahar sa jarabawa, duk wanda ya fadi ya sallame shi, kuma ya cike gurbin su da kwararru.
A Jahar Legos basa daukan malamin primary sai yana da B.Ed a subject din da a ke bukata.
Amma a Jihar Jigawa gwamnatin baya, ba ta dau mataki ba, sai dai cewa za a horar da malaman nan, har su sami kwarewa.
Rashin Isassun Malamai (Teacher Quantity)
Na fada a baya, ina tausayawa Malam a kan gadon da yayi na matsalar ilimi a Jigawa, musamman na karancin Malamai.
A watan October 2023, Shugaban Kungiyar Malaman Makaranta (NUT) ya ce, , Jahar Jigawa na fama da karancin Malamai 32,000. Yayi bayanin cewa yawan ritayar da malaman keyi ne ya jawo wannan matsalar, kuma gwamnati bata daukan sabbi.
Kiddiga ta nuna cewa, a bara ma Jigawa na da yawan daliban da ya kai 799,513, amma yawan malaman guda 14,776 ne. Kimanin Makarantu 210 wanda Malami daya kawai duke da shi. Makarantu 546 kuma Malamai biyu kachal suke da su.
Duba da wadannan matsalolin kachal, ya kamata muyi nazarin yaya za a warware su.
Malam Umar Namadi ya dauki alkawarin hidimtawa al’umar Jigawa kimanin Miliyan bakwai, zai inganta ilimin yayan su da ma basu ilimin.
Ya zama wajibi a yiwa Maigirma Gwamna da kuma wayanda suke rike masa amana adalcin yadda zasu magance wannan matsalar.
Tabbas ya zama wajibi a dauki malaman Makarantar da za su cike wannan gibin.
Duk da cewa, yanzu ba kawai Jigawa ba, a ma fadin kasar nan ana fama da matsin tattalin arziki, wanda ya hada da rashin aikin yi a tsakanin matasa, musamman Yan bokon da suka kammala karatun su, suna jiran samun aikin yi.
Amma fa dole sai an tantance wadanda za a dauke, bisa ilimi, dacewa da chanchanta, domin kaucewa matsalar farko da na fada a baya ta teacher quality.
Mu sani fa nauyin da ke kan gwamnati ba kawai daukan Malamai bane, bunkasa ilimi da Inganci sa a Jigawa shine dalili na farko, ya zama dole kenan gwamnati ta yi adalcin daukan ingantattun Malamai don ciyar da Jihar Jigawa gaba, da kuma kaucewa cin amanar daliban da kuma iyayen su.
Discussion about this post