Kotun majistare dake garin Jos babban birnin jihar Filato a ranar Litini ta yanke wa wasu matasa uku hukuncin zama a kurkuku na tsawon watanni uku bayan ta kama su da laifin fashi da makami.
Alkalin kotun Shawomi Bokkos ya yanke wannan hukunci ne wa Isah Paul mai shekara 22, Isah Daniel dan shekara 25 da Raphael Anthorny mai shekara 18 sannan ya kowanen su zabin biyan kudin belin naira 10,000.
Dan sandan da ya shigar da kara Ijuptil Thalwur ya ce wani Densen ne ya kawo kara ofishin ‘yan sanda dake Anglo-Jos ranar 16 ga Yuli
Thalwur ya ce Densen ya bayyana wa jami’an tsaron cewa wadannan matasa sun kawo musu hari inda suka nemi kwace wayoyi da wasu kaya masu daraja daga hannunsa da matarsa.
“Densen ya ce mutane sun kama matasan kafin su gudu sannan aka mika su ga ‘yan sanda.
Discussion about this post