Fitaccen ɗan wasan Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu ya yaba wa mawaki Davido bisa cire bidiyon batanci ga Musulunci da ya saka a yanar gizo.
Idan ba a manta tun bayan saka wani bidiyo da yayi da na wakar sa, da ke nuna wasu mutane suna rawa a gaban masallaci, wani a saman masallacin.
Tun bayan saka wannan bidiyo musulman Najeriya suka harzuka, suka nuna rashin jin daɗin su kan wannan bidiyo, da aka yi a masallaci
Abin ya jawo suka ga mawakin, da aka rika kira da ya cire wannan bidiyo a domin cin fuska ce ga musulunci karara.
Ali Nuhu ya ce abin da Davido ya yi cin fuska ce ga musulunci.
Bayan haka shima, Bashir Ahmad, ya soki abin inda ya yi kira ga Davido ya gaggauta cire bidiyon.
Bayan suka da mawakin ya sha daga mutane, ya cire bidiyon daga yanar gizo.
Discussion about this post