Shugabannin jaridar PREMIUM TIMES sun nesanta jaridar da kamfanin baki ɗaya daga sanarwar da wata ƙungiya ta yi, inda ta nuna cewa ta yi haɗin-gwiwa da wannan jarida domin bada lambobin karramawa ga wasu mutane.
PREMIUM TIMES na jawo hankalin jama’a cewa ba ta da wata alaƙa da ƙungiyar mai suna Hope Ambassadors for Peace in Africa, wadda ta shirya taron a ranar Talata.
‘Hope Ambassadors for Peace dai sun buga katin gayyata da wasiƙu waɗanda aka yaɗa a soshiyal midiya, masu ɗauke da cewa ƙungiyar za ta shirya karramawar da haɗin guiwar PREMIUM TIMES, inda a cewar su har ma da laccoci za a gudanar a wurin taron.
PREMIUM TIMES na sanar da jama’a cewa ba ta san da taron ba, kuma ba a shawarce ta ba kafin a maƙala sunan ta. Yadda kowa ya gani, ita ma sai jawo hankalin jaridar aka yi cewa an ga sunan ta cikin masu shirya tarone.
Saboda haka jama’a su yi watsi da wannan sanarwa, babu ruwan ta da taron.
PREMIUM TIMES mashahuriyar jarida ce da aka kafa sama da shekaru goma, mai hedikwatar ta a Abuja. Ta ginu a kan tsage gaskiya, bin ƙa’ida da kuma kare ƙimar ta da ƙimar aikin jarida a idon miliyoyin jama’a a ƙasar nan da ƙasashen duniya daban-daban.
PREMIUM TIMES sananna ce wajen nesanta kan ta da shiga duk wani shirgin da ba ta tantance sahihanci da nagartar sa ba. Kuma jarida ce da ta zama tamkar sautun doki, wanda ya fi ƙarfin a ce an je kasuwa an dawo, amma an manta ba a sayo ba.
Tuni dai masu shirya taron su ka bai wa PREMIUM TIMES haƙuri, bisa wannan kasassaɓa da su ka ɗibga ba da sanin jaridar ba. Kuma su ka tabbatar cewa za su cire sunan jaridar a cikin haɗakar masu shirya taron, wanda su ka shirya yi a ranar Talata, 23 Ga Mayu, kamar yadda su ka tabbatar a cikin wasiƙar neman afuwar da su ka aiko wa Babban Editan PREMIUM TIMES.
Shugaban Ƙungiyar mai suna Frank Chinedu ne ya sa wa wasiƙar hannu.
Discussion about this post