Melaye ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na gwamnan Kogi na jam’iyyar PDP
Sanata Dino Melaye na Jam’iyyar PDP ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP wanda aka yi a garin Lokoja ranar Lahadi.
Tsohon gwamnan Kaduna Sanata Ahmed Makarfi, da shine ya shugabanci zaɓen fidda gwanin ya bayyana sakamakon zaɓen kamar haka.
Melaye yayi nasara akan Ilona Kingsley da ya samu Kuri’u 124, Usman Kabiru da ya samu Kuri’u 121 da Abayomi Awoniyi, tsohon maraimakin gwamnan jihar da ya samu Kuri’u 77 kacal.
Sai kuma Wada Musa, da ya samu Kuri’u 56, Ojaja Enama, kuri’a 5, sai Olufemi Olarewaju da shima kuri’u 2 kacal ya samu.
Discussion about this post