Babban asibitin koyarwa na jami’ar Tafawa Balewa ATBUTH dake Bauchi ta bayyana cewa za ta fara tsarin IVF domin taimakawa ma’auratan da basu haihuwa a jihar.
Shugaban asibitin Yusuf Bara ya sanar da haka a taron kaddamar da farfajiyar tattaunawa tsakanin likita da marasa lafiya na asibitin da aka yi ranar Alhamis.
Bara ya ce ATBUTH ta hada hannu da asibitin ‘NISA Premier’ domin horas da jami’an asibiti kan wannan shiri IVF.
“Asibitin za ta hada hannu da kwararren likitan IVF Ibrahim Wada domin ganin shirin ya fara ya yadda aka tsara shi.
Ya kuma ce kwararrun jami’an lafiya daga ATBUTH da NISA za su hada hannu domin gano maganin cutar sikila wato ‘Sickle cell anemia’.
Bara ya tabbatar cewa wannan shiri da asibitin ta fiddo zai taimaka wajen rage cinkoson mutane a asibiti tare da samar wa marasa lafiya kulan da suke bukata.
Allah kin IVF hanya ce na yadda za a iya haɗa kwayayen halittar namiji da mace a waje bayan an dasa su sun fara haɗuwa kuwa halitta ta fara tabbata sai a saka shi cikin cikin mace.
Haga nan ta cigaba da ɗaukar sa har ta haifeshi.
Discussion about this post