Gwamnatin Kanada ta bayyana cewa ta na shirin karɓar masu hijira su na komawa ƙasar har mutum 1,450,000, waɗanda za ta bai wa katin zaman dindindin a ƙasar.
Ministan Harkokin Cikin Gida na Kanada, Sean Frazer ne ya bayyana haka a ranar Talata.
Ya ce an tsara karɓar masu hijira zuwa Kanada na wannan adadin daga 2023 zuwa 2025.
Wannan labari zai yi wa ɗimbin ‘yan Najeriya masu son ficewa daga ƙasar, domin Kanada ta na cikin ƙasashen da ‘yan Najeriya ke rububin zuwa, ko dai don su yi karatu, ko kuma neman aiki.
A cikin shekarun nan dubban ‘yan Najeriya sun gudu zuwa Kanada, Amurka da wasu ƙasashen Turai, saboda ƙoƙarin tsallake shingen matsin rayuwa da matsalar tattalin arziki a Najeriya da kuma gagarimar matsalar tsaro.
Fraser ya ce Firai Minista Justin Trudeau na so gwmnatin sa ta samar wa mutum 465,000 takardun shaidar zaman dindindin a Kanada a cikin 2023. Sai kuma cikin 2024 za ta yi marhabin da mutum 485,000, yayin da a cikin 2025 kuma ta karɓi wasu 500,000.
Wanann tsari dai ana so ne a samu ƙwararru a fannonin hada-hadar kasuwanci musamman ƙwararrun ma’aikata waɗanda za su samu aiki a cikin manyan birane, ƙauyuka da ƙananan garuruwan Kanada, domin tunkarar yadda za a magance kalubalen da tattalin arzikin ƙasar ke fuskanta, tsawon kusan shekaru goma kenan.
Discussion about this post