Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Kwanan nan, akwai wata magana da take yawo a kafar yada labarai ta intanet, wato soshiyal media, wanda aka danganta ga lauyan nan dan Najeriya, mai bincike akan al’amurran tsaro, wanda yanzu haka yake zaune a kasar Ingila, wato Barista Audu Bulama Bukarti, a inda aka ruwaito yace, “Baba (wato Shugaba Muhammadu Buhari) ko kansila bai kamata yayi ba, bare shugaban kasa.” Wannan magana, kafar soshiyal midiya mai suna IDON MIKIYA, sune suka wallafa ta, wadda suka yiwa matashiya da: ZARAR BUNU. Sannan bayan sun kawo maganar, sai suka yi tambaya a kasa, cewa, ME ZAKU CE?
‘Yan uwa, ga maganar nan zan kawo ta, ba tare da na canza komai ba, yace:
“Wato duk lokacin da ka saurari Baba sai ka ga dama can ko Kansila bai dace ya zama ba. Ni na rasa ma me muka gani tun farko har muka haƙiƙice cewa sai wannan bawan Allahn. Ba aiki a ƙasa, ba magana mai daɗi, ba tausayi, ba nadama kuma ba kunya, Cewar Barista Bulama Bukarti.”
To ni kuma da naci karo da wannan magana, na karanta, sai nayi sharhi kamar haka, nace:
Lallai biri yayi kama da mutum. Abun da yasa nace haka kuwa shine, domin a gaskiya Baba ko magana mai dadi, wadda shugaba zai yi, domin ya sanyaya wa talakawansa, akan irin ukubar da suke ciki ta rashin tsaro da talauci bai iya ba. Domin idan kun tuna, kwanan nan fa kafafen yada labarai suka ruwaito shi yana cewa, shi bai ga dalilin da zai sa ‘yan Nigeria suyi kukan talauci ko rashi ko yunwa ba, wai domin ga filayen noma nan a ko’ina, don haka mutane suje suyi noma!
Tambayar da zan fara da ita anan ita ce, shin don Allah kowa dai yasan cewa Baba yana da ‘ya ‘ya na jini ko? To a matsayin mu muma na ‘ya ‘yansa, kamar yadda har kullun yake irin wadannan maganganun, shin ‘ya ‘yan Baba na jini suna yin noma? Idan suna yi, to a ina ne gonakkin nasu suke? Sannan ko mutum yana so yayi noman, don Allah ina tsaron da zai bar shi yayi noman yake?
Alal misali, ni dan jihar Zamfara ne, don Allah yaje jihar Zamfara yaga irin yadda dubban mutane, bayin Allah, suke son suyi noma, kiwo ko kasuwanci, amma rashin tsaro ya hana su. An wayi gari talauci ya dabaibaye Zamfarawa, wallahi har ya bayyana a fuskokinsu. Duk inda ka shiga a cikin babban birnin jihar Zamfara babu abun da zaka gani sai mabarata, ban da dubban magidanta, masu iyali, wadanda basu da abunda zasu ci.
Ga rashin lafiya ta dabaibaye mutane, amma basu da kudin sayen magani. Mutane suna ta mutuwa da ciwo a jikin su, kasancewar basu da kudin zuwa asibiti.
Yanzu da nike wannan maganar ina nan Zamfara ne, cikin garin Gusau. Allah shine shaida, tun farkon damana, Zamfarawa basu yi noma ba sai da suka biya barayin daji wasu kudi domin su bar su suyi noman. Sannan yanzu sunyi noman, an kai ga amfanin, amma a halin yanzu kuma barayin daji sun ce babu wanda zai cire amfanin gonar sa. Wani yankin barayin daji sun sa masu haraji na miliyoyin kudi, kafin su bar su su cire amfanin gonar su, kudin da babu inda zasu samo su.
A jihar Zamfara wallahi babu wata rana da ba’a satar mutane maza da mata. Haka nan babu ranar da ba’a kisan bayin Allah. Kana kan tafiya baka tsira ba, kana gidan ka baka tsira ba, ka fito waje baka tsira ba.
A cikin watan nan, na rantse da Allah nasan mutane da dama, maza da mata wadanda aka sace, ban da wadanda aka kashe.
Jiya-jiyan nan juma’ah, 04/11/2022, wallahi aka yiwa wani mutum yankan rago a kusa da anguwar mu. A gaban mutane, kowa yana kallo. ‘Yan banga/’yan sakai ne suka yanka shi. Sun ce wai informer ne, wato wanda yake tare da barayin daji, yana fada masu sirrin mutane, suna zuwa suna daukar su domin karbar kudin fansa.
A halin yanzu abun ya kara rikicewa a jihar Zamfara. An bar mutane a hannun Allah. Ana iya shiga ko’ina a dauki mutum, kawai sai wanda Allah ya kiyaye. Sai dai muna addu’a da rokon Allah ya kawo muna dauki, amin.
Wannan magana da nike fada, idan ba gaskiya bane, zan tsaya gaban Allah gobe Alkiyama in amsa tambayoyi a gaban Allah! Ko kuma idan ba gaskiya bane, ina bukatar wani wanda yake cikin jihar ya fito ya karyata ni, yace ba haka bane!
Talauci, yunwa, rashin tsaro, masifu iri-iri, daban-daban, duk gasu nan sun addabi al’ummah.
Talakawa muji tsoron Allah, mu koma ga Allah, mu gyara tsakanin mu da Allah, mu gyara halayen mu da mu’amalolin mu, mu ci gaba da istighfari, da addu’a da rokon Allah da yawaita sadaka, domin Allah ya tausaya muna, ya kawo muna saukin wannan jarabawa. Domin wallahi jarabawa ce wadda hannayen mu suka jawo muna.
Shugabanni su kuma suji tsoron Allah, kar su manta fa, sun yi rantsuwa, sun dauki alkawarin kare rayukan talakawa da dukiyoyinsu. Kuma su sani, wallahi zasu mutu, zasu tsaya gaban Allah, Allah zai tambayesu akan zubar da jinin talakawansu da ake yi a koda yaushe. Wadanda Allah ya damka amanar Zamfarawa a hannun su dole ne su zage damtse wurin tunkarar wannan jarabawa!
Sannan ya zama wajibi a kyautata mu’amala tsakanin talakawa da shugabanni. Wannan lamari ne wanda yake bukatar hada hannu domin shawo kansa. Akwai bukatar hada karfi da karfe wurin tunkarar wannan jarabawa. A daina zage-zagen juna, a daina zagin shugabanni. Shugabanni su daina musgunawa talakawansu. Su daina kama talakawansu suna daure wa, domin sun fadakar dasu akan matsalar jihar. Wannan lamari wallahi kowa akwai inda ya kasa, don haka duk mu hadu mu gyara, sai Allah ya dube mu da idon rahama!
Shugabanni, ‘yan siyasa da masu arzikin jihar Zamfara ya zama dole ku fitar da kayan arziki domin amfanin talakawanku; ku raba matasa da bangar siyasa, ku samar masu da aikin yi, ko Allah zai tausaya, ya kawo muna karshen wannan ibtila’i, idan kuma da gaske ne kuna so wannan matsalar ta kare.
Kun sani, ni dan jihar Zamfara ne gaba-da-baya. Ni dan Gusau ne har iyaye da kakanni. Duk abunda yake faruwa na sani. Barnar da ake yi a jihar Zamfara wallahi tayi yawa. Da yawan matasan mu sun zama ‘yan luwadi (homosexuals), mata sun zama ‘yan madigo (lesbians), sai wadanda Allah ya kare. Zinace-zinace ko’ina. Barayi ko’ina. Kai a jihar Zamfara har ta kai ga an samu mace da namijin da suka yi jima’i a filin Allah, a cikin tashar mota, a gaban mutane, kowa yana kallo, babu kunya babu tsoron Allah. Wai domin su nuna wa mutane cewa su ‘yan iska ne. A jihar Zamfara ne bokaye da ‘yan siyasa suka hada kai suna jefa Alkur’ani, maganar Allah cikin masai/ shadda/ toilet, duk domin neman duniya.
Iyaye suna bayar da hayar ‘ya ‘yansu mata ga barayin daji, domin su kwanta da su a biya su kudi, saboda talauci da rashin imani da rashin tsoron Allah! ‘Yan kasuwa, masu kudi da manoma basu fitar da hakkin Allah na Zakkah daga dukiyoyinsu! A koda yaushe, lokaci bayan lokaci, ana gano gidajen tsafe-tsafe daban-daban a cikin jihar Zamfara! Shaye-shaye a wurin matasan mu, maza da mata, da gidajen shaye-shaye da wuraren sayar da kwayoyi sun yi kamari a duk fadin jihar Zamfara.
A gaba na, na tafi asibitin Ahmad Sani Yariman Bakura (Specialist hospital), aka kawo mutane jina-jina, an sassaresu, an kashe wasu, duk da sunan siyasa, tsakanin magoya bayan ‘yan siyasa. ‘Yan siyasar mu sun mayar da matasan mu ‘yan daba, ‘yan sara-suka, ‘yan turowe a duk fadin jihar, alhali su ‘ya ‘yansu duk suna makaranta suna karatu.
Jihar da take ikirarin dabbaka Shari’ar Musulunci, amma gidajen fasikanci da masha’a duk sun dabaibaye jihar. Gidajen da ake fitsara gasu nan ko’ina. Matan aure zina, ‘yan mata zina, zawarawa zina. Abun sai dai ace inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!
Kuma duk wannan fa ina mai tabbatar maku da cewa, suna faruwa ne saboda jefa al’ummah cikin mugun fatara da talaucin da yunwa da aka yi.
Mu a jihar Zamfara, Allah ya jarrabe mu da matsalolin shugabanci. Duk wani ci gaba da idan ka tafi wata jiha zaka gani, mu a jihar Zamfara babu. Roko, bara, maula da banbadanci sun zamanto wani kayan ado a jihar Zamfara!
Shin don Allah, duk wannan bala’i da yake faruwa a jihar Zamfara, kawai sai Allah ya kyale mu, don yana tsoron mu, ba zai jarabe mu ba? Mu tuna fa, Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tabbatar muna da cewa DUK ABUNDA MUKA GANI NA MUSIBU DA BALA’O’I DA JARABAWA, TO HANNAYEN MU NE SUKA JEFA MU CIKI! Kuma Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tabbatar muna da cewa, BA ZAI TABA DAUKE SU, KO YA CANZA MUNA BA, HAR SAI MUN DAINA ABUNDA MUKE YI MARAR KYAWO!
Mu sani, bala’i baya sauka sai da zunubi, kuma Allah baya dauke shi sai da tuba, istighfari da komawa ga Allah!
Kuma mu sani, su shugabanni, Allah yana bamu su ne irin yadda muke ko yadda muka kasance. Idan mun zama na kirki sai Allah ya bamu shugabanni na kwarai. Idan kuma mun zama mutanen banza, sai Allah ya bamu shugabanni ‘yan iska. Da ma ance: ” KAMA TAKUNU YUWALLA ALAIKUM.” Ma’ana yadda kuke haka Allah yake baku shugabanni.
Sannan Allah yace: KAMAR HAKA MUKE DORA AZZALUMAI AKAN AZZALUMAI IRIN SU, SU DANDANA MASU AZABA.”
Haka ‘yan uwana Zamfarawa, mu sani, tun daga mataki na kasa, har na jiha, wallahi idan muna son Allah ya bamu shugabanni na gari, to mu gyara halayenmu.
Shi shugaba yaji tsoron Allah, ya sauke nauyin da Allah ya dora masa, su kuma talakawa su sauke nasu nauyin da Allah ya dora masu. Idan mun yi haka, In Shaa Allahu, Allah zai tausaya muna.
Amma maganar gaskiya shine, kowa da laifin sa, kuma kowa da irin gudummawar da zai bayar domin cimma abun da muke bukata.
Amma gaskiyar magana, wallahi jihar Zamfara abun babu kyau.
Kuma dole ne muga laifin Baba Buhari, domin a jihar Zamfara rashin tsaro, yunwa da talauci sun addabi al’ummah, amma shi kawai yana ganin cewa laifin mutane ne, tun da wai basu yin noma. Alhali suna son suyi noman, amma maganar shine, ina tsaron yake?
Allah ya sawwake, ya kawo muna mafita, amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau. 08038289761.
Discussion about this post