Ɗaya daga cikin waɗanda ƴan bindiga suka saki cikin waɗanda suka sace a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna Amina, ta gudanar da zangazangar gwamnati ta kara kaimi wajen tattaunawa da ƴan bindiga su saki mijinta da ke tsare a hannun ƴan bindigan.
Amina wacce ta fito ita kaɗai rike da rubutu a takarda da ke yin kira ga gwamnati su saki mijinta ta ce bata iya barci tunda ta dawo daka daji.
” Tunda aka sako ni ba na iya barci, idan na tuna mijina na can tsare a daji tare da ƴan bindiga. Don Allah ku taimake ni gwamnati ta kara kaimi wajen gqnin Maharan sun sako sauran waɗanda ke tsare a hannun su.
Amina ta ce dukkan su da ke tsare a can wurin maharan ba su da lafiya, wasu ma sun makance ba su gani, wasu sun rasa hannayen su da waau sassan jikin su saboda rashin lafiya.
Idan ba a manta ba a cikin wannan mako shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su gaggauta sannan su ƙara ƙaimi wajen ganin an ceto sauran mutanen da ke tsare a hannun ƴan bindigan.
Garkuwa da mutane a Najeriya musamman yankin Arewa ya yi tsanani da a kullum sai an samu rahoton an sace mutane ko kuma an kashe su.
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya umari ƴan jihar su mallaki bindigogi domin su kare kansu.
Discussion about this post