Gidauniyar Ɗan takarar gwamnan jihar Kano AA Zaura Foundation ta sanar da ware wasu har naira miliyan 200 domin tallafawa ɗalibai ƴan asalin jihar Kano dake manywn makarantun kasar nan.
A sanarwar wanda Daily Nigerian ta buga a yanar gizo, Zaura ya ce wannan ɗaya ne daga cikin alƙawurran da yayi a sakon sa na sabuwar shekara da yayi wa mutanen jihar Kano.
” Sanin kowa ne ilimi shine ginshikin zaman duniya, a dalilin haka ne zan tallafawa ɗalibai ƴan asalin jihar Kano 10,000 da tallafin naira 20,000 kowannen su.
” Mun samar da fom din da za a cika zassauƙi ba tare da an wahala ba. Bayan haka kuma akwai tallafi da Gidauniyar AA Zaura zai baiwa mata da kungiyoyi fon cigaban al’umma a jihar Kano.
Bi nan domin samun wannan tallafi: https://aazaura.org.ng/education-support-fund/
Discussion about this post